Isa ga babban shafi

Farashin tikitin jirgin ya ninka a Najeriya

Rahotanni daga najeriya na cewa a halin yanzu kamfanonin jiragen saman kasar na ci gaba da karin farashin tikiti, yayin da suka dora alhakin hakan da hauhawar farashin man jirgin, si dai kuma masana na danganta hakan da karancin jiragen.

Jirgin sama mallakin Najeriya, yayin kaddamar da soma aikinsa daga filin jirgin saman birnin Legas. 18/9/2009.
Jirgin sama mallakin Najeriya, yayin kaddamar da soma aikinsa daga filin jirgin saman birnin Legas. 18/9/2009. REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Kamar yadda bayanai ke cewa tashin farashin tikitin baya ga nasaba da tsadar man jirgin, haka zalika faduwar darajar kudin kasar ya taka rawa.

Kungiyar masu jiragen sama a kasar, ta yi hasashen cewa daga nan zuwa 2023, ana iya samun tsaikon jigilar jiragen sama na kamfanoni uku sakamakon kalubalen da suke fuskanta.

Latsa alamar sauti domin sauraron rahoton Shamsiyya Haruna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.