Isa ga babban shafi

Faransa ta kaddamar da shirin bunkasa harshen Faransanci a Lagos

Yau Faransa ke kaddamar da wani shirin bunkasa koyar da harshen Faransanci a makarantun Lagos da ke kudancin Najeriya, karkashin wata yarjejeniya da za a sabunta tsakanin gwamnatin jihar da karamar ministan raya kasa da dangantaka tsakanin kasashen a Faransa.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. © MICHAL CIZEK / AFP
Talla

A ziyarar da ta ke yi yanzu haka Najeriya tun daga ranar 28 ga watan Mayu, uwargida Chrysoula Zacharopoulou ta halarci bikin ranstsar da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu kafin ta karasa jihar Lagos don aiwatar da shirin koyar da harshen na Faransanci. 

Bikin sanya hannu kan yarjeniniyar, wata dama ce ta sake tabbatar da kawancen da aka yi a baya da kuma kaddamar da sabon shirin koyar da harshen Faransaci a makarantun sakandiren gwamnati a zamanance. 

Kafin bikin da zai gudana yau a birin Legas, sai da karamar ministan ta Faranasa da ke kula da cigaba da kuma dangantar kasa-da-kasa da kuma raya harshen Faransanci ta kai ziyara birnin Ilori na jihar kwara, inda suka sanya hannun kan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin jihar kan ayyukan gona da raya al’adu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.