Isa ga babban shafi

Najeriya: Ruftawar gini ya kashe wasu yara biyu a jihar Legas

Wasu yara biyu masu suna Gbolahan da Olayinka Atolagbe sun mutu bayan da wani katangar  wani gini da ke makwabtaka da su ya rufta a gidansu a unguwar Ikorodu dake jihar Legas.

Vivre à Lagos
Vivre à Lagos © RFI / Studio graphique
Talla

Rahotanni suka ce lamarin ya faru ne a wannan asabar  lokacin da ake ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a anguwar.

An tsinto gawarwakin yaran biyu ne bayan da kwashe sa'o'i a karkashin baraguzai duk da kokarin mazauna anguwar da suka kai musu daukin gaggawa.

Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen Kudu-maso-Yamma, Mista Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar.

Jihar Legas ta yi kaurin suna wajen ruftawar gine-gine wanda so tari kan kai ga tasa rayukan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.