Isa ga babban shafi

An sauke hakimi a Katsina sabida daurin aure

Tsohon hakimin Kuraye da ke karamar hukumar Charanchi a jihar Katsina, Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu, ya mayar da martani kan murabus din da masarautar Katsina ta yi masa.

Tsohon Hakimin Kuraye da ke jahar Katsina.
Tsohon Hakimin Kuraye da ke jahar Katsina. © Daily Trust
Talla

Hakimin wanda ke rike da sarautar Sarkin Kurayen Katsina, a jiya Litinin ne dai aka sanar da dakatar da shi daga matsayinsa, sabida jagorantar daurin auren wasu ma'aurata da daya daga cikinsu ke dauke da cuta kanjamau.

A cikin sanarwar da sakataren yada labaran gwamnan jahar Katsina Abdullahi Aliyu Yar’adua ya fitar, ta ce gwamnatin Jahar ta dauki matakin ne bisa shawarwarin da masarautar Katsina ta ba ta, ya yinda a gefe guda kuma masarautar ta ce an masa murabus ne bisa umarnin gwamnatin Jahar.

Toh sai a martanin da tsohon hakimin na Charanchi Alhaji Abubakar ya mayar, ya ce ya kafin ya jagoranci daura auren, sai da ya kai ma’auratan wajen likitoci da kuma hukumar da ke kula da cutar sida ta Jahar don basu shawarwari.

A cewarsa, bayan cika dukkanin ka’idodin da suka kamata, ciki harda sanya hannu a yarjejeniyar amincewa da dukkanin sharudan da aka shimfida da kuma irin magungunan da ya kamata mijin ya rinka amfani da su da likitoci suka bayar, hakan ya sa ya jagoranci daura musu aure.

Toh sai dai jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ce, babu wani karin bayani kan ko anbaiwa basaraken damar kare matakin nasa kafin sauke shi daga sarautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.