Isa ga babban shafi
Zamfara-Najeriya

Gwamnatin Zamfara a Najeriya ta dakatar da hakimai 4

Rahotanni daga Jihar Zamfara da ke Najeriya na nuna cewar Gwamnatin Jihar ta dakatar da wasu masu rike da mukaman sarautar gargajiya guda 4 da ake zargin cewar suna alaka da Yan bindigar dake kashe jama’ar Jihar.

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari.
Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari. rfi hausa
Talla

Kwamishinan kula da kananan hukumomi da masarautu, Bello Dankande ya ce sarakunan sun hada da Hakimin Gora da ke Talatar-Mafara da Hakimin Barikin Daji.

Sauran sun hada da Mai garin Gyado da Tungan Dutsi da ke karamar hukumar Bukkuyum.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan sarakunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.