Isa ga babban shafi

Najeriya: Jami’ai a Zamfara sun sahalewa ‘yan bindiga zuwa aikin Hajji - Rahoto

Rahotan wani bincike ya nuna yadda jami’an kwamitin Hukumar Hajjin bana ta 2023 na Jihar Zamfara suka sahalewa wasu sanannun 'yan ta'adda da gangan damar zuwa aikin hajjin da aka kammala a kasar Saudiyya.

Gwamnan jihar Zamfara kenan, wato Dauda Lawal Dare.
Gwamnan jihar Zamfara kenan, wato Dauda Lawal Dare. © dailytrust
Talla

Rahoton ya kuma zargi wasu daga cikin jami’an da yin almubazzaranci da kudade, da rashin samun cikakkun takardu daga maniyyata da kuma rage kudin alawus-alawus na alhazai da sauran ayyukan rashawa.

Jaridar Premium Times da ake wallafa a Najeriya tace hakan na zuwa ne makonni biyar bayan da ta labarta wani rahoto na musamman kan yadda jami’an tsaro suka cafke ‘yan ta’adda da matansu da kuma wasu masu yi wa ‘yan ta’adda aiki a filin jirgin saman Sultan Abubakar III da ke Sokoto bayan dawowarsu daga kasar Saudiyya.

Kwamitin aikin hajjin shekarar 2023 da gwamnatin jihar ta kaddamar, a wani cikakken rahoton da ya yi nazari kan aikin da aka kammala, ya mika wa gwamnan jihar, Dauda Lawal, rohotan a ranar Alhamis.

Jami'in da ya kwarmatawa jaridar labarin, yace kwamitin ya shawarci gwamnati da a yi garambawul ga hukumar alhazai ta jihar (ZAHCOM).

Rahotanni sun ce shugaban kwamitin Musa Mallaha ya shaida wa gwamnan cewa baya ga barin masu aikata laifuka su shiga aikin hajjin bana, jami’an hukumar ZAHCOM sun kuma kirkiro hanyoyi daban-daban na karkatar da kudaden gwamnati da na alhazai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.