Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe mutane 34 a Zamfara

Jami’an tsaron sa-kai na ‘yan banga sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 34 ciki har da sojoji 7, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya
Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya © Daily Trust
Talla

Shugaban jami’an tsaron sa kan yankin Dan Gulbi Ismail Magaji ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ‘yan ta’addan sun kai hari kan gundumar da ke karamar hukumar Maru ne da yammacin ranar Litinin.

Wani mazaunin garin ya ce mutane 27 da bakwai ‘yan bindigar suka kasha, yayin da kuma suka kashe wasu sojoji 7 bayan kwanton Baunar da suka yi musu a lokacin da jami’an tsaron ke kan hanyar kai wa mutanen da aka kai wa farmakin dauki.

Zamfara dai na daga cikin jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya da ‘yan bindiga ke kai hare-hare tare da satar mutane domin karbar kudin fansa, lamarin da yayi sanadin salwantar rayukan mutane da dama, da kuma hasarar dimbin dukiya, gurgunta noma da kuma harkokin kasuwanci a wasu yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.