Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun fatattaki gungun 'yan ta'adda a Zurmi

Rahotanni daga yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce rundunar sojin saman Najeriya, ta yi nasarar fatattakar gungun ‘yan ta’adda a yankin Zurmi da ke jihar Zamfara.

Jirgin yakin Najeriya
Jirgin yakin Najeriya © Daily Trust
Talla

Yayin harin da dakarun Najeriya suka kai a ranar Asabar, sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga 16 daga cikin gungun da suka tarwatsa, sai dai jagoransu da yayi kaurin suna wajen ta’addanci mai suna Dankarami, da aka fi sani da Gwaska ya tsallake rijiya da baya tare da  munanan raunuka.

Kafar watsa labarai ta Intanet ta PRNigeria, ta ruwaito wata majiya na cewa gabanin farmakin jiragen yakin Najeriyar, kasurgumin dan ta’adddan ya yi ta kokawa kan kudurin sojojin Najeriya na kawar da shi da iyalansa.

Bayanai sun ce sai da jiragen yakin Najeriya suka shafe sa’o’i suna ruwan bama bamai kan sansanin Dankarami, kamar yadda kakakin rundunar sojin saman Najeriya Edward Gabkwet, ya tabbatar.

Dankarami da aka fi sani da Gwaska dan asalin karamar hukumar Zurmi a Zamfara, wanda ya yi kaurin suna wajen ta’addanci a yankunan arewacin jihar ta sa da kuma yankunan yammacin jihar Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.