Isa ga babban shafi

Zamfara za ta dauki mayakan sa kai dubu 2 don yaki da 'yan bindiga

Gwamnatin Zamfara ta amince da daukar sabbin mayakan sa kai dubu 2 don shiga cikin rundunar yaki da ‘yan bindigar wadda gwamnatin jihar ke tafiyarwa a kokarin baiwa jama’a cikakkiyar kariya daga batagarin.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Shugaban kwamitin da ke kula da dakarun masu yaki da ‘yan bindigar a Zamfara Mr Bello Bakyasuwa a jawabinsa gaban manema labarai jiya Alhamis a birnin Gusau, ya ce sun karbi umarnin daga Gwaman Bello Matawalle game da daukar sabbin ‘yan sakan.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawalle ne ya yi umarnin kafa kwamitin na musamman don yakar matsalolin ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi.

A cewar Bello Bakyasuwa akalla mutane dubu 6 da 700 suka mika takardun neman aikin a sassan jihar ciki har da mata said ai duka-duka mutum dubu 2 za a dauka don gudanar da aikin.

Jihar Zamfara na sahun jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.