Isa ga babban shafi

Harin 'yan bindiga ya kashe mutum 15 a Sokoto da Zamfara dake Najeriya

Akalla mutane 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da ‘yan ta’adda suka mamaye al’ummomin jihohin Zamfara da Sokoto da yammacin ranar Litinin, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Rahotanni daga kasar na cewa, garuruwan da maharan suka farwa, sun hada da Ruwan Bore a Zamfara da Gatawa, Dangari da Kurawa a Jihar Sakkwato.

A Sokoto, lokacin da maharan suka shiga cikin mutane, yawancin mazauna garin sun gudu zuwa wasu kauyuka.

An kashe mutane hudu yayin da wasu sama da 10 suka samu raunuka daban-daban.

A Dangari, ‘yan ta’addan sun je yankin Gatawa da Kurawa duk a karamar hukumar Sabon Birni, inda suka farwa mutane da harbe-harbe.

Jaridar Premium times ta ruwaito cewa, a daren ranar Litinin, mutane 11 ne suka mutu daga yankunan uku, inda da dama suka jikkata sosai.

Zamfara

A jihar Zamfara gungun ‘yan ta’addan sun kai hari a unguwar Ruwan Bore da ke Gusau babban birnin jihar, inda suka kashe wasu mutane hudu tare da jikkata wasu 10.

‘Yan bindigar sun shiga garin da yammacin ranar Litinin, inda suka rika harbin kan ‘uwa dawabi, inda suke dauke da Babura sama da 100.

Mata da kananan yara da dama ne suka tsere kauyen Kwatarkwashi domin tsira da rayukansu, yayin da mazan garin suka fake a wasu wuraren domin binne gawarwakin da aka bari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.