Hajji 2023: An sanya Hausa cikin harsunan da za'a fassara hudubar ranar Arafat
Mahukunta Masallatan Alfarma na kasar Saudiyya, sun sanya Hausa a cikin jerin harsuna 20 da za a yi amfani da su wajen fassara hudubar ranar Arafa ta bana. Daidai lokacin da mahajjata a sassan duniya suka fara aikin sauke farali na bana a kasar mai tsarki.
Wallafawa ranar:
Shafin Haramain Sharifain ne ya tabbatar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook jiya Asabar.
A shekarun bayan nan dai an rika fassara hudubar ranar Arafa cikin harsuna daban-daban, inda kusan shekaru uku da suka gabata harshen hausa ya samu shiga.
Hajjin bana
A wannan Lahadin ne ake soma aikin hajjin a Makkatul Mukarrama cikin yanayin zafi, inda dubun dubatar musulmi suka halarci aikin hajjin farko da aka baiwa kowa dama a masarautar tun bayan barkewar cutar Covid-19.
Sama da mahajjata miliyan biyu daga kasashe 160 ne ake sa ran zasu gudanar da Ibadan na bana a birnin mafi tsarki ga addinin musulunc a yammacin Saudiya, bayan shafe shekaru uku ana takaita adadin masu halarta saboda barkewar annobar korona.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu