Isa ga babban shafi

Mahajjatan Najeriya sun samu karin wa'adin isa Saudiya

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Saudiyya (GACA) ta tsawaita wa’adin maniyyan Najeriya daga ranar 4 ga watan Yuli zuwa 6 ga watan Yuli.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tawagarsa a Masallacin Ka'aba na Saudiya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tawagarsa a Masallacin Ka'aba na Saudiya. © Daily Trust
Talla

Mataimakiyar Darakta a sashen hulda da jama’a na hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) Misis Fatima Usara ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja.

Ta ce matakin ya zama dole, saboda tsaikon da ya wuce kima da ake samu a filin jiragen saman na tsawaita wa’adin tashi da saukar jiragen.

Jinkirin jirage

Ta ce daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuni an soke tashin jirage akalla tara.

Wannan, a cewarta, ya biyo bayan wasu dalilai da suka hada da gazawar wasu hukumomin alhazai na Jihohi na biyan Alawus din Basic Travel Allowance (BTA) ga mahajjata, rashin isassun kudade don biza da kuma rashin samun sakamakon gwajin PCR.

Wadanda aka kwashe

Hukumar tace daga cikin mahajjatan Najeriya 43,008 da ake sa ran su iso kasar Saudiyya, 27,359, da suka hada da ma’aikata 527 da kwamitoci da shugabannin hukumar da ke karkashin kason gwamnati ne suka isa kasa mai tsarki yanzu haka.

Mahajja miliyan 1

Mahukunta a Saudiyya, sun ce mahajjata milyan daya ne za su gudanar da aikin hajjin bana, wato daya daga cikin shika-shikan addinin musulunci biyar, sabanin miliyan biyu da dubu 500 da suka gudanar da irin wannan ibada a shekara ta 2019.

Mahajjata dubu 850 za su kasance ‘yan asalin kasashen ketare, kuma zuwa ranar Lahadi 650 sun isa kasar a cewar mahukuntan Saudiyya,  yayin da wasu dubu 150 za su kasance ‘yan asalin kasar ta Saudiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.