Isa ga babban shafi

Mutane 11 suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota

Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta ce mutane 11 sun mutu sakamakon wani mummunan hatsari tsakanin motoci uku, da ya rutsa da su akan babbar hanyar da ta tashi daga garin Ore zuwa Benin a jiya.

Vue générale de l'accident de la route survenu le 16 janvier 2023, près de Sakal, dans le nord du Sénégal.
Vue générale de l'accident de la route survenu le 16 janvier 2023, près de Sakal, dans le nord du Sénégal. © Ousseynou Diop/AFP
Talla

Mutane 19 da suka hada da maza 10, da mata 8 da kuma wata karamar yarinya guda hatsarin ya shafa da safiyar jiya Alhamis, daga cikinsu ne kuma 11 suka rasa rayukansu, yayin da 8 suka jikkata.

Hukumar kiyaye hadurran Najeriya ta FRSC ta ce hatsarin ya rutsa ne da motoci da suka hada da Karama guda, da Bas da kuma Tirelar kamfanin Dangote, kuma rashin kyawun birkin daya daga cikin motocin ne ya janyo mummunan hatsarin.

Hadurran ababen hawa musamman tsakanin motoci na cigaba da  zama sila mutuwar dimbin mutane a Najeriya.

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar ta taba fitar sun nuna cewar  a shekarar 2020, kimanin mutane 5,574 ne suka rasa rayukansu, yayin da rayukan wasu 6,205 suka salwanta a shekarar 2021. 

Alkaluman sun kuma nuna cewar mutane 1,834 ne suka mutu a cikin hadurran da yawansu ya kai 3,345 a titunan Najeriya a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar bara ta 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.