Isa ga babban shafi

Maniyyatan farko a Najeriya sun yi hatsari a kan hanyar su ta zuwa filin jirgi

Wata mota dauke da maniyyata daga jihar Nassarawa sun yi hatsari, yayin da ssuke kan hanyar su ta zuwa filin jirgin saman Abuja babban birnin kasar, domin zuwa kasa mai tsarki.

Maniyatan da suka gamu da hatsari a Najeriya
Maniyatan da suka gamu da hatsari a Najeriya © BNN
Talla

Motar mai daukar mutum 18 ta yi hatsarin ne a daidai kauyen Kara, da ke yankin karamar hukumar Keffi.

Rahotanni basu bayyana cewa ko an samu asarar rai ba, amma wasu daga cikin maniyyatan sun samu rauni.

Jihar Nassarawa ce za a fara diban maniyyatan farko a Najeriya, inda za su tashi daga Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.