Isa ga babban shafi

Hukumar alhazan Najeriya ta sanar da karin farashin Hajin bana

Hukumar Alhazan Najeriya tayi amai ta tande dangane da karin kudin hajin bana, inda ta sanar da karin Dala 100 ga duk wani maniyyacin da zai gabatar da aikin hajin wannan shekara. 

Musulmi yayin gudanar da sallah a masallacin Ka'aba da ke birnin Makka.
Musulmi yayin gudanar da sallah a masallacin Ka'aba da ke birnin Makka. REUTERS - Waleed Ali
Talla

Sanarwar da hukumar ta gabatar yace sabon matakin ya biyo bayan rikicin da ake ci gaba da yi a kasar Sudan, abinda ya tilastawa jiragen da za suyi jigilar maniyata kaucewa bi ta sararin samaniyar kasar da kuma tsawaita tafiyar. 

Hukumar tace karin da aka samu yanzu ya kai na Dala 250 akan kowanne maniyacci, amma kuma tayi nasarar shawo kan kamfanonin jigilar maniyatan yin ragi, yayin da za’a ragewa kowanne maniyaci kudin alawus da za’a bashi daga Dala 800 zuwa Dala 700. 

Idan baku manta ba, lokacin da kamfanonin jigilar maniyatan suka ki sanya hannu akan kwangilar aikin, mun tintibi Daraktan dake kula da jigilar maniyatan Abdullahi Hardawa wanda yace suna can suna nazari akan hanyoyin da ya dace abi wanda ba zai kaiga maniyata sun biya Karin kudi ba. 

Wannan rikici na Sudan yayi sanadiyar kaucewa sararin samaniyar kasar ga duk maniyatan da zasu tashi daga yankin Afirka ta Yamma, abinda ya sa sai an bi ta karin wasu kasashe, kuma bisa ka’idar sufurin jiragen sama, sai wadannan kamfanonin sun biya haraji ga duk kasar da zasu ratsa sararin samaniyarta. 

Akalla maniyata dubu 75 ake saran su sauke farali daga Najeriya a wannan shekarar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.