Isa ga babban shafi

Fasinjoji 17 sun kone kurmus a hatsarin mota a Abuja

Kimanin fasinjoji 17 ne suka kone kurmus bayan motarsu ta yi hatsari wadda ta taso daga jihar Gombe domin zuwa jihar Lagos da ke kudancin Najeriya.

Ana yawan samun hatsarin motoci a Najeriya, lamarin da ke haddassa salwantar rayuka da dama.
Ana yawan samun hatsarin motoci a Najeriya, lamarin da ke haddassa salwantar rayuka da dama. © Tribune
Talla

Rahotanni na cewa, mummunan hatsarion ya auku ne a tskanin babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja a sanyin safiyar yau Talata.

Daya  daga cikin mutanen da suka shaida lamarin, Kabiru Garba, ya bayyana cewa, motar kirar Toyota Hiace mai kujeru 18 ta ci karo ne da wata katuwar motar dakon kaya a kusa da marabar Yaba, akan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Garba ya kara da cewa, motar bus din ce ta manno a guje ta kuma ci karo da katuwar motar ta baya, lamarin da ya sa busa din ta kama da wuta nan take.

Tuni jami’an kwana-kwana suka isa wurin da hatsarin ya auku domin kashe wutar da ta tashi, yayin da a gefe guda, jami’an kiyaye hadurra na FRSC ke aikin ceto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.