Isa ga babban shafi

Sakin Kanu ne zai samar da zaman lafiya a Kudu maso Gabashin Najeriya-Soludo

Gwamnan jahar Anambra da ke shiyar Kudu maso Gabashin Najeriya Charles Soludo, ya ce ya na neman a saki jagoran kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra IPOB Nnamdi Kanu ne, don warware matsalolin tsaron da ke damun yankin su.

Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo.
Gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo. © Daily Trust
Talla

Soludo ya sake jaddada cewar a shirye ya ke ya tsaya wa Kanu idan har gwamnatin Tarayyar kasar za ta bada shi beli.

Gwamnan ya ce ya rubutawa shugaban kasar mai barin gado Muhammadu Buhari bukatar sakin Kanu, kuma ya ce a shirye ya ke ya ci gaba da wannan fafutuka wajen gwamnati mai jiran gado idan har wannan gwamnati ta gaza wajen bada belin sa.

Soludo ya ce ci gaba da tsare Kanu na daga cikin dalilan da ke kara ta’azara matsalar tsaro a yankin su, don haka ya ce a damka Kanu a hannun sa, lamarin da ya ke ganin zai samar da zaman lafiya.

A watan Yunin shekarar 2021 ne dai aka sake kama Nnamdi Kanu a kasar Kenya, aka kuma sake maida shi Najeriya bayan karya ka’idojin belin sa da aka bayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.