Isa ga babban shafi

Kotu ta bukaci gwamnatin Najeriya ta mayar Nnamdi Kanu Kenya

Wata kotu a Najeriya ta umurci gwamnatin kasar da ta dauki shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu ta mayar da shi kasar Kenya inda ta dauko shi ba tare da bin ka’ida.

Nnamdi Kanu Shugaban kungiyar IPOB a  Najeriya
Nnamdi Kanu Shugaban kungiyar IPOB a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde/Files
Talla

Mai shari’a a kotun tarayya dake birnin Umuahia, Evelyn Anyadike ta gabatar da wannan hukunci, yayin da ta bukaci gwamnati da ta biya Kanu diyyar naira miliyan 500 saboda cin zarafinsa da tayi.

Lauyoyin Kanu suka shigar da kara a kotun inda suke neman a bi musu kadi akan kama shi da jami’an gwamnatin Najeriya suka yi a kasar Kenya ba tare da bin doka ba da kuma dauko shi zuwa Najeriya, bayan ya gudu daga belin da aka bada shi.

Mai shari’a Anyadike tayi nazari akan hukuncin kotun daukaka karar da ta saki Kanu a Abuja ranar 13 ga wannan wata wajen amincewa da bukatun guda 8 da ya gabatar mata wadanda suka kunshi biyan diyyar da kuma mayar da shi kasar Kenya inda aka same shi.

Anyadike ta bayyana cewar, yadda aka kama Kanu aka ci zarafinsa da tsare shi da kuma kin bada shi beli ya nuna karara yadda aka take hakkinsa.

Lauyan Kanu, Alloy Ejimakor ya jinjinawa mai shari’ar akan wannan hukuncin wanda yace ya tabbatar da zaman kotu a matsayin wadda ke kare hakkin wadanda aka cuta.

Lauyan ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta mutunta wannan hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.