Isa ga babban shafi

Nnamdi Kanu: Muna farin ciki da hukuncin kotun koli - Ohanaeze

Kungiyar Dattawan ‘Yan Kabilar Igbo dake Njaeriya ta Ohanaeze ta bayyana matukar farin cikin ta da hukuncin kotun koli wanda ya wanke Nnamdi Kanu daga tuhumar da ake masa na cin amanar kasa tare da bada umurnin sakin sa kai tsaye.

Nnamdi Kanu Shugaban kungiyar IPOB a  Najeriya
Nnamdi Kanu Shugaban kungiyar IPOB a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde/Files
Talla

Mai magana da yawun kungiyar Chidozie Ogbonnia yace hukuncin kotun ya dada daga darajar Najeriya da kuma karfin dimokiradiyarta a idan duniya.

Ogbonnia yace hukuncin kotun ya haifar da matukar farin ciki a yankin kudu maso gabashin Najeriya, saboda yadda shari’ar da ake yiwa Kanu ta jefa yankin cikin fargaba da tashin hankali, sakamakon irin tashe tashen hankulan da ake samu da kuma tilastawa mutane zaman gida kowacce litinin.

Kungiyar ta yabawa alkalan kotun daukaka kara da suka yanke hukuncin sakin Kanun saboda jajircewar da suka yi wajen yanke wannan hukunci mai matukar tasiri. Wannan hukunci ya raba kan jama’ar Najeriya da dama, musamman masana harkar shari’a inda wasu ke bayyana shakku dangane da matsayin da alkalan kotun suka dauka na yanke irin wannan hukunci na watsi da tuhume tuhumen da ake yiwa Nnamdi Kanu wadanda suka shafi cin amanar kasa da kuma tsallake belin da aka bashi.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyar ta na daukaka kara akan hukuncin da kuma ci gaba da sauran shari’un da ake yiwa Nnamdi Kanu na cin amanar kasa.

Bayan wani taron majalisar tsaron kasa da akayi jiya juma’a, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ministan ‘Yan Sanda Maigari Dingyadi ya sanar da cewar gwamnati bata amince da hukuncin kotun daukaka karar ba, saboda haka zata daukaka kara a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.