Isa ga babban shafi

Kotun daukaka kara a Najeriya tace a ci gaba da tsare Nnamdi Kanu

Kotun daukaka kara da ke Abujan Najeriya, ta amince da dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke na gurfanar da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu bisa zargin ta’addanci.

Shugaban kungiyar IPOB
Shugaban kungiyar IPOB REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Gwamnatin Tarayya, ta yi ikirarin cewa an sallami Kanu, amma ba a wanke shi ba, kuma ta garzaya kotu domin ta dakatar da aiwatar da hukuncin sakin.

Kotun daukaka kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke wanda ya shafi mayar da Kanu daga Kenya zuwa Najeriya tare da ajiye tuhumar da ake masa na ta'addanci.

A ranar Juma’a ne kwamitin alkalai mai mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Haruna Tsamani ya bayyana cewa zai dace a jira karar zuwa gaban kotun koli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.