Isa ga babban shafi

Gwamnoni 7 da ke kan mulki sun gaza samun kujerun Sanata a zaben Najeriya

Gwamnonin Najeriya 7 masu ci ne suka gaza samun nasarar zabensu zuwa majalisar dattawan kasar a zaben da ya gudana a karshen mako, sakamakon shan kayen da suka yi a hannun abokan karawarsu. 

Zauren tattara sakamakon zaben Najeriya.
Zauren tattara sakamakon zaben Najeriya. © Voice of Nigeria
Talla

Wadannan gwamnoni sun hada da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da Bem Ayade na Jihar Cross Rivers da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da kuma Darius Ishaku na Jihar Taraba. 

Sauran sun hada da darakta janar na yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, wato gwamnan jihar Filato Simon Lalong da takwaransa na jihar Benue Samuel Ortom. 

Wasu daga cikin tsoffin gwamnonin da suka rasa damar komawa majalisar dattawan sun hada da Kabir Ibrahim Gaya na jihar Kano da Tanko Almakura na jihar Nasarawa, da Gabriel Suswam na Benue da Sam Egwu na Ebonyi, sai kuma tsoffin gwamnoni irinsu Ibrahim Hasssan Dankwambo da Abdulaziz Yari da Godswill Akpabio da suka samu nasara. 

Daga cikin wadanda suka samu nasara kuma akwai David Umahi da Abubakar Sani Bello. 

Masana na bayyana sakamakon wannan zabe a matsayin yadda jama’a suka nuna fushinsu akan rashin gamsuwa da ayyukan da wadannan mutane suka yiwa jama'a a wa'adin mulkinsu da ke shirin karewa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.