Isa ga babban shafi

An ci zarafin ‘yan jarida 14 yayin watsa labaran zaben Najeriya - CPJ

'Yan jarida da sauran ma’aikatan kafafen watsa labarai akalla 14 ne aka tsare, ko kuma aka kai musu hari, a yayin da suke daukar rahotannin zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokokin Najeriya.

Na'urar daukar magana a dakin watsar labarai
Na'urar daukar magana a dakin watsar labarai © REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Kwamitin kare hakkin ‘yan jarida na kasa da kasa CPJ, ya ce daga cikin manema labaran da aka ci zarafin nasu har da mai shafin intanet na WikkiTimes mai zaman kansa, Haruna Mohammed Salisu, wanda ke ci gaba da zama tsare a hannun ‘yan sanda ba tare da tuhumarsa ba,

Bayanai sun ce ‘yan sanda sun tsare Salisu ne tun a ranar 25 ga watan Fabrairu a garin Duguri da ke kudu maso gabashin jihar Bauchi, jim kadan bayan da shi da wasu ‘yan jarida suka gana da gwamnan jihar, kamar yadda editan WikkiTimes Yakubu Mohammed, wanda ya zanta da kwamitin CPJ, da wata gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida na cikin gida ya bayyana.

Sai dai ‘Yan sandan da ake zargi sun ce sun kama Salisu ne domin kare shi bayan da magoya bayan gwamnan suka kai masa hari a lokacin da yake hira da matan yankin da ke zanga-zangar, amma sai suka ki sakin shi, a cewar Mohammed, wanda ya ziyarce shi bayan an mayar da shi hedikwatar ‘yan sanda da ke Bauchi, inda yake tsare har zuwa daren ranar Litinin din da ta  gabata.

Kwamitin kare hakkin ‘yan jaridun na duniya CPJ, ya  kara da cewar baya  ga  Haruna Muhammad, kungiyoyin siyasa, da kuma jami'an tsaro sun yi barazanar kai hari, ko kama wasu 'yan jarida da ma'aikatan watsa labarai akalla 13 yayin zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayyya da suka gudana ranar 25  ga watan Fabarairu.

Daya daga cikin manema labaran da suka fuskanci wannan cin zarafi dai shi ne Dayo Aiyetan, babban daraktan cibiyar tattara rahotanni mai zaman kanta ta kasa da kasa, wanda wasu gungun mutane sun lakadawa duka tare da, yaga tufafinsa, baya ga sace wayarsa, saboda kawai ya dauki dauki hotonsu a daidai lokacin da suke kokarin hana kada kuri’a a wata  rumfar zabe da k birnin Abuja.

Aiyetan ya ce mutum daya ya yi kokarin daba masa wuka, daga bisani kuma bayan kai wa ‘yan sanda rahoto, an dawo da wasu daga cikin kayansa, har da wayarsa bayan goge muhimman abubuwan da ke cikinta.

A garin Ibadan kuwa, wasu matasa sun kai hari ne kan wata motar kamfanin dillancin labarai na Najeriya da ke aikin tattara rahotannin zaben, kamar yadda daya daga cikin manema labaran da lamarin ya rutsa da su ya shaida wa CPJ.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.