Isa ga babban shafi

Legas: IPC ta yi Allah wadai da cin zarafin mawallafin Wikki Times

Kungiyar 'Yan Jaridu ta Duniya reshen jihar Lagos dake Najeriya ta yi Allah wadai da matakin da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta dauka cin zarafin mawallafin Jaridar Wikki Times Haruna Mohammed da wakilinsa Idris Kamal.

'Yan jarida yayin wata zanga-zangar ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya a birnin Lagos, babban birnin kasuwancin Najeriya, 3 ga Mayu, 2010.
'Yan jarida yayin wata zanga-zangar ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya a birnin Lagos, babban birnin kasuwancin Najeriya, 3 ga Mayu, 2010. © REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Rahotanni sun ce an ci zarafin ‘Yan Jaridun guda biyu ne lokacin da suka amsa gayyatar jami’an tsaro zuwa ofishin ‘Yan Sandan dake gudanar da bincike sakamakon korafin da Dan Majalisar wakilai Yakubu Shehu Abdullahi yayi akan su dangane da rahotan mutuwar shugaban Jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Bauchi.

Kungiyar ta ce bayan amsa gayyatar da ‘Yan Jaridun suka yi sai Yan Sanda suka tsare su na sa’oi 10 tare da cin zarafin su abinda ya kaiga yi musu raunuka a jikin su jiya litinin kafin su sake su tare da umurni komawa ofishin Yan Sandan yau talata.

IPC ta ce bayan sun kai kansu yau Talata, sai Yan Sandan suka kai su kotu inda aka tuhume su da laifin bata suna, abinda ya sa alkali ya bada umurnin tsare su har zuwa gobe laraba.

Shugaban Kungiyar Lanre Arogundade ya bayyana matukar damuwar su dangane da wannan al’amari, inda ya janyo hankalin Rundunar Yan Sandan Jihar Bauchi da ta daina barin Yan siyasa suna amfani da ita wajen biyan bukatar kan su.

Arogundade ya bukaci jami’an tsaro su dinga amfani da dokar kasa wajen gudanar da hakkin su ba tare da cin zarafin manema labarai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.