Isa ga babban shafi

Zaben shugaban kasa: Atiku ya doke abokan hamayyarsa a Osun

Dan takarar babbar jam’iyyyar adawa ta PDP a zaben shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Osun.

Dan takarar kujerar shugaban Najeriya na jam'iyyyar PDP Atiku Abubakar.
Dan takarar kujerar shugaban Najeriya na jam'iyyyar PDP Atiku Abubakar. (AP Photo/Manuel Balce Ceneta)
Talla

Bayan samun nasara a kananan hukumomi 20 daga cikin 30, sakamako ya nuna cewar Atiku ya lashe kuri’u 354,366 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 343,945 bayan samun nasara a kananan hukumomi 10.

Dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar na jihar Osun da jimillar kuri’u 23,283, sai Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da ya samu kuri’u 713.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.