Isa ga babban shafi

INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa

Hukumar zabe ta INEC a Najeriya ta ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa bayan dakatar da aikin karbar sakamakon daga jihohi a jiya lahadi.

Zauren tattara sakamakon zaben Najeriya
Zauren tattara sakamakon zaben Najeriya © Voice of Nigeria
Talla

Hukumar zabe ta INEC a Najeriya ta ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa bayan dakatar da aikin karbar sakamakon daga jihohi a jiya lahadi.

Tun da misalin karfe 11 na safiyar yau ne hukumar ta INEC ta fara karbar sakamakon zaben don kammala fitar da hakikanin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan da muke ciki na Fabarairu.

Sai a yau ne dai INEC za ta fara karbar sakamakon zaben na jihohi bayan da ofisoshinta daga sassan kasar suka kammala tattara sakamakon zaben duk da cewa har yanzu akwai sauran jihohin da basu kammala hada sakamakon zabensu a cikin gida ba.

Al’ummar Najeriya dai na ci gaba da zuba ido don ganin wanda zai maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari dai dai lokacin da sakamakon zaben a wasu yankunan kasa ke ci gaba da bayar da mamaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.