Isa ga babban shafi

Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa a Kwara

Dan takarar kujerar shugabancin Najeriya na jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya lashe mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar da ya gudana a jihar Kwara.

Bola Tinubu dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyyar APC.
Bola Tinubu dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyyar APC. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sakamakon da hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar, ya nuna cewar daga cikin kuri’un da aka kada, Sanata Tinubu ya samu kuri’u 263,572, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu kuri’u 136,909.

Dan takarar jam’iyyar Labour Party LP, Peter Obi ne ya zo na uku, bayan samun kuri’u 31,166.

Ana sa ran mika sakamakon zaben zuwa cibiyar hedikwatar hukumar INEC da ke Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.