Isa ga babban shafi

Sanata Kabiru Gaya ya amince da shan kaye zaben wakilcin Kano ta Kudu

Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, Ibrahim Kabiru Gaya, na jam’iyyar APC ya rasa kujerar wakilcin da yake a zauren majalisar dattijai bayan shan kaye a hannun dan takarar jam’iyyar NNPP, Abdulrahman Kawu Sumaila.

Tsaffin Gwamnonin jihar Kano, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da kuma Sanata Malam Ibrahim Shekarau
Tsaffin Gwamnonin jihar Kano, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da kuma Sanata Malam Ibrahim Shekarau © Twitter/@shekarau60
Talla

A sakamakon da hukumar zabe INEC ta sanar, jam’iyyyar APC ta samu kuri’u 10,079, yayin da NNPP ta samu kuri’u 18,419, sai kuma PDP da ta zo uku bayan samun kuri’u 747.

Tuni dai Sanata Ibrahim Kabiru Gaya ya bayyana amincewa da sakamakon zaben cikin wani sakon muryarsa da aka nada, inda ya taya abokin hamayyarsa Kawu Sumaila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.