Isa ga babban shafi

'Yan sanda a Kano sun tabbatar da kisan magoya bayan jam'iyyar NNPP

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 3 tare da jikkatar da dama, bayan barkewar wani rikici tsakanin magoya bayan wasu jam’iyyun siyasa a yankin karamar hukumar Tudun Wada.

Rabi'u Musa Kwankwaso, dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar NNPP a lokacin kada kuri'arsa.
Rabi'u Musa Kwankwaso, dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar NNPP a lokacin kada kuri'arsa. AP - Sani Maikatanga
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sanda jiya SP Abdullahi Kiyawa ya shaidawa wakilinmu Abubakar Isa Dandago cewa biyu daga cikin wadanda suka mutu a rikicin ‘yan daba ne suka kone su kurmus bayan da suka farwa ofishin jamiyyar su da ke yankin yayin da guda kuma ya rasa ransa lokacin da jami’an tsaro suka kawo dauki dan kwantar da rikicin.

A cewar sa da misalin karfe 4 na yammacin jiya ne lokacin da ake tattara sakamakon zabe a Ofishin INEC tawagar 'yan daba ta rufarwa ofishin jam'iyyar NNPP tare da sanya wuta wanda ya hada da mutanen biyu wadanda ke cikin mota a harabar Ofishin.

Kakakin ya ci gaba da cewa tuni aka kame mutane 4 cikin masu hannu a wannan ta'annati wadanda za su girbi abin da suka shuka.

Abdullahi Kiyawa ya ce yanzu haka kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi umarnin fara wani sumame don lalubo wadanda ke hannu a tashin hankalin.

Ana ci gaba da zaman dar-dar a jihar ta Kano da ke arewacin Najeriya, musamman lura da yadda manyan jam’iyyun siyasa da suka kunshi APC da NNPP da kuma PDP ke ci gaba da watandar kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar da ya gudana a Asabarb din nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.