Isa ga babban shafi

NNPP ta tsayar da Kwankwaso a matsayin dan takararta

Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta bayyana tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin dan takarar zaben shugaban kasar shekara mai zuwa.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Premium Times
Talla

Taron jam’iyyar na kasa da ya gudana a birnin Abuja ya amince da takarar Kwankwaso da kuma wasu yan takarar gwamnonin jihohi da zasu shiga zabe mai zuwa.

Kwankwaso ya bukaci Yan Najeriya da su basu goyan baya wajen kawar da jam’iyyar APC daga karagar mulki saboda abinda ya kira gazawar da tayi wajen samar da tsaro da kuma ci gaban kasa.

Tsohon gwamnan ya sha alwashin kawo sauyi da kuma samar da ci gaban da jama’a ke bukata muddin jama’ar Najeriya suka basu amanar jagoranci a zaben shekara mai zuwa.

Kwankwaso ya bayyana Jam’iyyar NNPP a matsayin wadda ta sha banban daga sauran manyan jam’iyyun kasar da suka ci amanar jama’a wajen kin gabatar musu da ayyukan raya kasa da kuma ci gaban da ake bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.