Isa ga babban shafi

Yadda fitattun 'yan siyasa suka rasa kujeru da mazabunsu a zaben 2023

Sakamakon zaben ‘yan Majalisu na ci gaba da bayar da mamaki lura da yadda ‘yan takarar da ba sanannu ba ke ci gaba da kwace kujerun fitattun ‘yan Majalisu, a bangare guda ‘yan takarar shugaban kasar ke shan kaye a yankunan da suka saba mamayewa.

Sakamakon zabe na ci gaba da bayar da mamaki a sassan Najeriya.
Sakamakon zabe na ci gaba da bayar da mamaki a sassan Najeriya. AP - Ben Curtis
Talla

Sakamakon da INEC ke ci gaba da bayyanawa na nuna yadda Bola Ahmed Tunibu dan takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki APC ya gaza kawo jihar shi, wadda Peter Obi na Labour ya lashe yayinda Atiku Abubakar ya lashe jihar Katsina mahaifar shugaba Muhammadu Buhari.

Can a jihar Kano Sanata Kabiru Gaya na jam’iyyar APC da ya shafe shekaru 16 a zauren Majalisar dattijai ya sha kaye a hannun Abdurrahman Kawu Sumaila daga jam’iyyar NNPP.

Shi ma gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya gaza kawo karamar hukumarsa wadda NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso ta lashe.

A bangare guda shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya gaza kawo rumfarsa a jihar Nassarawa wadda ta fada hannun Labour yayinda Ahmed Wadada na jam’iyyar SDP ya lashe kujerar sanatan yankin.

Sanata a Cross River ta arewa Jarigbe Agom Jarigbe na jam’iyyar PDP ya kayar da Gwamna Ben Ayade na APC wajen sake darewa kujerar dan majalisar dattijai.

A bangare guda Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da ke jam’iyyar PDP ya rasa kujerar shi ga jam’iyyar Labour.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.