Sabuwar girgizar kasa ta sake afkawa gabashin Turkiyya
Wata sabuwar girgizar kasa mai karfin maki 5.6 ta sake afkawa yankin gabashin Turkiya yau litinin inda ta kashe mutum guda tare da jikkata dubbai baya ga rushe tarin gidaje.
Wallafawa ranar:
Girgizar kasar ta yau litinin na zuwa ne kwanaki 7 bayan makamanciyarta da ta sake afkawa sassan kasar bayan mummunar girgizar kasar ranar 6 ga watan Fabarairu da ta kashe mutane kusan dubu 50 a kasar da makwabciyarta Syria.
Sanarwar da hukumar kare afkuwar bala’o’I ta kasar ta fitar ta ce baya ga mutum guda da ya mutu akwai kuma wasu 69 da suka jikkata yayinda gidaje 29 suka rushe.
Hukumar ta ce jim kadan bayan afkuwar girgizar kasar, jami’anta suka isa yankunan da ibtila’in ya faru don kai dauki wannan dalili ne ya rage samun asarar rayuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu