Isa ga babban shafi

Jonathan ya yi watsi da fom din takarar da aka saya masa karkashin jam'iyyar APC

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nesanta kan sa daga wadanda suka ce sun saya masa fom domin tsayawa takarar shugaban kasar zaben da za a yi a shekara mai zuwa a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Wata sanarwar da mai magana da yawun sa Okechukwu Eze ya rabawa manema labarai ta ce Jonathan bashi da wata masaniya dangane da saya masa takardar takarar kuma bashi da wata alaka da wadanda suka ce sun saya.

Sanarwar ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da rahotanni cewar zai tsaya takara a Jam’iyyar APC duk da ya ke sun san cewar wasu daga cikin kiraye kirayen da ake wa tsohon shugaban na da matukar tasiri.

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a yayin mika mulki ga Muhammadu Buhari a 2015.
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a yayin mika mulki ga Muhammadu Buhari a 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde TPX IMAGES OF THE DAY

Tun farko dai wata kungiyar ‘yan arewacin Najeriya da ake dangantawa da Fulani ce ta sanar da biyan Jam’iyyar APC naira miliyan 100 domin karbar fom din takarar zaben shugaban kasar da sunan Goodluck Jonathan, matakin da ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Najeriya.

Ko a kwanakin baya sai da wasu matasa su ka yi zanga zangar lumana a Abuja babban birnin Najeriyar wadanda suka yi tattaki zuwa ofishin Jonathan tare da bukatar shi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben na 2023.

Zuwa yanzu mutane sama da 25 suka sayi tikitin tsayawa zaben karkashin APC ciki har da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da ministan Mai Timipriye Sylva.

Gwamnan Bauchi kuma tsohon ministan Birnin Abuja a karkashin Jonathan da yanzu haka ya ke takarar neman tikitin PDP domin tsayawa zaben shugaban kasar, ya ce muddin Jonathan ya bayyana aniyar sa ta tsayawa, zai yi watsi da na shi takarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.