Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SIYASA

Rashin halartar Jonathan taron PDP ya haifar da cece kuce

Rashin halartar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan taron kasa na Jam’iyyar PDP da aka kammala a karshen wannan makon, ya dada jefa shakku dangane da makomar sa, yayin da ake ci gaba da rade radin cewar zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Rahotanni sun ce tsohon shugaban ya sanar da tafiyar sa zuwa Nairobi Kenya domin halartar taron tsaro da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afirka ta AU, sai dai wasu ‘yan jam’iyyar basu gamsu da uzurin da ya gabatar ba, inda suke cewa wani dalili ne kawai na kin halartar taron.

Jaridar Premium Times tace Gwamnan Bayelsa Douye Diri da takwaran sa na Oyo Oluseyi Makinde sun yi iya bakin kokarin su wajen janyo hankalin shugaban wdomin ganin ya halarci taron a ranar juma’ar da ta gabata amma hakar su bata cimma ruwa ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali. © Presidency of Nigeria

Jaridar tace Gwamnonin biyu sun bayyana aniyar su ta samawa Jonathan wani jirgi na daban da zai kai shi Nairobi idan ya halarci taron na PDP amma tsohon shugaban yaki amincewa da bukatar su.

Premium Times ta nemi ji daga bakin mai magana da yawun Jonathan Ikechukwu Eze wanda ke tare da shi a Nairobi dangane da kin halartar taron amma kuma abin yaci tura.

Rahotanni da dama na bayyana yadda wasu daga cikin jiga jigan Jam’iyyar APC ke kokarin shawo kan hankalin Jonathan domin komawa Jam’iyyar APC da zummar bashi takara a shekara mai zuwa.

Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari lokacin da suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2015.
Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari lokacin da suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2015. Reuters

Daga cikin masu nuna wannan sha’awa harda wasu daga cikin gwamnonin APC dake adawa da takarar jagoran su Bola Ahmed Tinubu a shekara mai zuwa.

Gwamnan Jihar Rivers Nyesome Wike ya taba janyo hankalin tsohon shugaban a baya cewar kada ya kuskura yayi kuskuren komawa Jam’iyyar APC domin matakin zai shafi kimar sa.

Ya zuwa wannan lokaci Jam’iyyar APC ta fada cikin rikicin cikin gida abinda ya kaiga samun rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yayan ta, inda aka samu bangarori da dama a zaben shugabannin jihohin da akayi.

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan yayin yakin neman zabe a shekarar 2015.
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan yayin yakin neman zabe a shekarar 2015. AP - Sunday Alamba

Wannan na daga cikin barakar da ake ganin zata iya yiwa Jam’iyyar illa a zabe mai zuwa, bayan rigimar inda ‘dan takarar shugaban kasa na shekarar 2023 zai fito.

A shaguben da ya yiwa APC bayan kammala taron da akayi a karshen wannan mako, sabon shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu yace APC ba zata iya gudanar da taron kasa ba, domin kuwa lokacin da ta gudanar da taron jihohi, shugabanni 92 aka samu a Jihohi 36, abinda ke nuna gazawar jama’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.