Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP na gudanar da babban taron zaben sabbin shugabanni

Mambobi da wakilan babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun hallara a dandalin taro na Eagles Square da ke birnin Abuja domin gudanar da babban taronsu na kasa don kuma zabar sabbin shugabanni.

Wani taron 'yan babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.
Wani taron 'yan babbar Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya. © Daily Trust
Talla

Babban taron da zai gudana a yau da gobe na da muhimmanci matuka ga babbar jam’iyyar adawar wajen tunkarar babban zaben shekarar 2023 a Najeriya.

Manya da kanan Jami’an jam’iyyar ta PDP na kasa, gwamnoni, tsofaffin gwamnoni, da sauran jiga-jigan jam’iyyar ne dai ke halartar taron zaben sabbin shugabannin.

Rahotanni sun ce za a cike mafi yawan mukaman da za a yi takara akansu ne ta hanyar cimma matsayar fahimtar juna.

Kafin wannan taron dai babbar jam'iyyar adawar ta sha fama da rikicin cikin gida da takun saka ta fuskar shari'a, inda tsohon shugaban ta Uche Secondus ya nemi kotu ta hana taron, saboda dakatar da shi daga jam’iyyar.

Amma a ranar Juma’a, Kotun daukaka kara da ke birnin Fatakwal a Jihar Rivers ta bai wa jam’iyyar damar gudanar da babban taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.