Isa ga babban shafi
Najeriya - PDP

Iyorchia Ayu ya zama sabon shugaban jam'iyyar PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta kammala taronta na kasa a birnin Abuja da sanyin safiyar yau Lahadi inda aka zabi Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugabanta.

Iyorchia Ayu sabon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.
Iyorchia Ayu sabon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya. © Qed.ng
Talla

Daga cikin jawabin da ya gabatar, Ayu ya sha alwashin cewa jam’iyyar ta dawo domin karbe mulki daga hannun APC mai mulki, wadda ya zarga da jefa Najeriya cikin halin kaka ni kayi.

A gefe guda yayin taron da aka kammala Ambasada Umar Iliya Damagum ya doke tsohuwar ministar harkokin mata kuma shugabar mata ta PDP ta kasa Hajiya Inna Ciroma, wajen darewa matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar Arewa.

Babban jami’in zaben gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin shirya taron jam’iyyar PDP na kasa ne ya sanar da sakamakon, inda yace Damagum ya samu kuri’u dubu 2, da 222 inda ya doke Ciroma da ta samu kuri’u 365.

Babban taron na PDP dai na da matukar muhimmanci gare ta dangane da shirin babban zaben shekarar 2023 a Najeriya.

Kafin taron dai babbar jam'iyyar adawar ta sha fama da rikicin cikin gida da takun saka ta fuskar shari'a, inda tsohon shugaban ta Uche Secondus ya nemi kotu ta hana taron, saboda dakatar da shi daga jam’iyyar.

Amma a ranar Juma’a, Kotun daukaka kara da ke birnin Fatakwal a Jihar Rivers ta bai wa jam’iyyar damar gudanar da babban taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.