Isa ga babban shafi
Najeriya - siyasa

Secondus ya ci gaba da matakin hana gudanar da taron PDP

Tsohon shugaban babbar jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya Prince Uche Secondus ya garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara reshen Fatakwal ta yanke, wanda ta amince jam’iyyar ta ci gaba da babban taron na kasa da zai gudana a Abuja yau din nan.

Uche Secondus tsohon shugaban rikon kwaryar jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
Uche Secondus tsohon shugaban rikon kwaryar jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya © Rfi hausa
Talla

Tuni shirin babban taron jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya kankama a Abuja babban birnin ƙasar, inda ake sa ran ƴaƴan jam'iyyar daga ko ina a faɗin kasar su zaɓi manyan shugabanninta.

PDP ta samu wannan damar, bayan kotu tayi watsi da bukatar da wasu ‘ya’yan jam'iyar suka shigar   kotu domin a dakatar da gudanar da taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.