Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SIYASA

Yadda za'a hada kan 'Yan Najeriya - Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bada shawarar hanyoyin da ya dace abi wajen samun dunkulalliyar kasa mai cike da zaman lafiya.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan AP - Baba Ahmed
Talla

Jonathan wanda ya bayyana cewar Allah Ya wadata Najeriya da arzikin jama’a da kuma albarkatu daban daban, ya kara da cewar za’a ci gajiyar su ne kawai idan an samu dawwamammen zaman lafiya a cikin kasar.

Tsohon shugaban ya bukaci shugabanni da su mayar da hankali wajen gina hadin kan kasa da yin adalci ga kowanne bangare ba tare da fifita wata kabila ko jama’a akan wata ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali. © Presidency of Nigeria

Jonathan yace babban kalubalen dake gaban shugabanni shine hada kan jama’ar kasa, kuma hakan ba zai samu ba muddin ana fifita wata al’umma ko kabila akan wata ba.

Tsohon shugaban yace muddin aka fifita wata kabila ko al’umma akan wata, za’a samu rashin hadin kai da kuma korafe korafe daga wadanda aka hana su hakkokin su na ‘Yan kasa.

Magoya bayan Nnamdi Kanu
Magoya bayan Nnamdi Kanu AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI

Kalaman tsohon shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da wasu kabilu da yankunan Najeriya ke korafi akan nuna musu banbanci da kuma hana su mukaman da suka ce ya dace a basu.

Daga cikin masu korafin akwai ‘Yan kabilar Igbo dake kudu maso gabashin kasar wadanda ke cewa an hana su rike daya daga cikin manyan ofisoshin tsaron kasar, a matsayin daya daga cikin korafin da masu fafutukar kafa kasar Bifra ke amfani da shi wajen bayyana dalilin yunkurin da suke na samun kasa ta kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.