Isa ga babban shafi
Najeriya

Babbar kotun Najeriya ta ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Babbar kotun Najeriya dake birnin Abuja ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, matakin da ya biyo bayan bukatar hakan da gwamnatin tarayyar kasar ta gabatarwa babbar kotun.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Cikin kudirin da ta gabatar, gwamnatin Najeriya ta ce rahotannin tsaro sun tabbatar da alhakin kashe-kashe, da satar mutane don karbar kudin fansa, da aikata fyade, da sauran nau’ikan ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabas, arewa ta tsakiya da sauran sassan kasar nan da ‘yan bindigar ke yi.

Yayin tsokaci kan matakin, ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami, ya ce hukuncin kotun ya karfafi aniyar gwamnati ta murkushe ‘yan bindigar, ta hanyar daukar tsauraran matakai akansu fiye da kowane lokaci.

Sai dai fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriyar Shiekh Ahmad Gumi ya bayyana rashin amincewarsa da matakin ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda, abinda ya dade yana gargadin cewa, zai iya haifar da karin matsaloli a maimakon warware wadanda ake ciki.

Malamin dai ya dade yana kiran da gwamnati ta samar da shirin yi wa ‘yan bindigar afuwa, matakin da ya ce shi ne mafi sauki wajen warware matsalolin tsaron da suka addabi jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.