Isa ga babban shafi
NAJERIYA-NOMA

Manoman Najeriya na amfani da maganin kwarin da aka haramta a Turai - Rahoto

Wani bincike a Najeriya yace manoman kasar na amfani da magungunan kashe kwari masu matukar illa wadanda aka haramta sayar da su ko amfani da su a kasashen Turai saboda illar da suke yiwa Bil Adama.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Binciken da kungiyar dake yaki da maganin kwari a gonaki ta gudanar wanda ya samu tallafin kungiyar Heinrich Boll Stiftung yace kashi 40 na magungunan kashe kwarin da ake amfani da su a gonakin Najeriya tuni aka haramta amfani da su a kasashen Turai.

Rahotan binciken da akayi a Jihohin Kano da Oyo da Ebonyi da kuma Benue yace adadin kashi 40 din da aka gabatar na nuni ne da kashi 57 na nau’in abincin daban daban da suka kai kala 402 da ake nomawa a cikin Najeriya.

Irin tattasai da kayan yajin da ake nomawa a Najeriya
Irin tattasai da kayan yajin da ake nomawa a Najeriya © Mercedes Ahumada

Binciken yace akasarin maganin kwarin na dauke da sinadaran dake matukar illa ga rayuwar Bil Adama da dabbobi da kuma muhalli.

Rahotan yace kashi 25 na magungunan kwarin da aka yiwa rajista a Najeriya na da sinadarin dake iya haifar da cutar kansa ko kuma sankara, yayin da kashi 63 na da sinadarin dake haifar da cuta a jikin Bil Adama, sai kuma kashi 47 da ke dauke da sinadarin dake haifar da matsala a jinin Bil Adama.

Wata mata na amfani maganin Roudup na kamfanin Monsanto wajen kashe kwarin da ke cinye amfanin gona
Wata mata na amfani maganin Roudup na kamfanin Monsanto wajen kashe kwarin da ke cinye amfanin gona REUTERS/Benoit Tessier

Binciken yace magungunan kwarin 262 na dauke da guba, yayin da 224 suka nuna yadda suke haifar da matsalar rashin haihuwa.

Rahotan masanan yace an gano illar da irin wadannan magunguna kan yiwa muhalli lura da yadda mutane 270 suka mutu sakamakon gurbata ruwan su da irin wannan maganin kashe kwarin da aka haramta amfani da shi a nahiyar Turai ya yiwa mutanen Jihar Benue.

Wani manomi na aikin a gonar sa a Najeriya
Wani manomi na aikin a gonar sa a Najeriya Fati Abubakar/RFI

Jaridar Premium Times ta ruwaito masanan na bada shawarar cewar ya dace majalisar dokoki ta kasa ta kaddamar da bincike akan matsalar da zummar yin dokar da zata takaita amfani da irin wadannan magungunar dake yiwa jama’a da muhalli illa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.