Isa ga babban shafi
AFIRKA-NOMA

Matsalolin dake hana matasa rungumar noma a Afirka - Heifer

Wani binciken masana da Kungiyar Heifer International ta gudanar ya bayyana cewar manoma a nahiyar Afirka basa samun damar da ta dace na amfani da sabbin na’urorin zamani wajen bunkasa aikin noman da suke yi, abinda ke hana su samun ci gaban da ake bukata.

Wani manomi akan motar tantan yayin aiki a gonarsa dake jihar Nasarawa a Najeriya.
Wani manomi akan motar tantan yayin aiki a gonarsa dake jihar Nasarawa a Najeriya. © Alluvial Agriculture/Handout via Reuters
Talla

Rahotan kungiyar Heifer International da akayi nazari a kasashe 11 dake nahiyar Afirka ya gano cewar rashin samun na’urorin zamani wajen tafiyar da harkar noman da kudade da kuma horarwar da ta dace na matukar illa ga bangaren noman da samar da abinci.

Rahotan da aka yiwa lakabi da 'makomar aikin noma da kuma rawar da matasa ke takawa wajen amfani da na’urorin zamani‘ ya biyo bayan tambayoyin da aka yiwa matasa kusan 30,000 tare da daruruwan manoma da kungiyoyin su a kasashen da suka hada da Habasha da Kenya da Najeriya da Ghana da Senegal da kuma Tanzania.

Wata 'yar kasar Mali yayin noman zamani na gida da ake kira da 'Greenhouse Farming' a turance, a gonarta dake garin Katibougou.
Wata 'yar kasar Mali yayin noman zamani na gida da ake kira da 'Greenhouse Farming' a turance, a gonarta dake garin Katibougou. © REUTERS/Annie Risemberg

Binciken ya gano muhimmancin tallafawa matasa da kudade domin rungumar aikin noman domin samar da ayyukan yi da farfado da hanyoyin samar da abinci wanda annobar korona ta yiwa matukar illa.

Adesuwa Ifedi, mataimakiyar shugabar Heifer International tace nahiyar Afirka dake dauke da tarin matasa na bukatar inganta bangaren noma wajen zuba jarin da zai janyo hankalin matasa sun rungumi aikin domin wadata jama’a da abinci.

Ifedi ta bayyana takaici da yadda ake samun koma baya wajen samar da kudade da kuma zuba jari da horarwar da ta dace wajen samar da manoman dake amfani da sabbin dabarun zamani domin bunkasa noman da ake bukata.

Manoma a wata gona dake kauyen Asipa Ila a wajen Abeokuta dake kudu maso yammacin Najeriya.
Manoma a wata gona dake kauyen Asipa Ila a wajen Abeokuta dake kudu maso yammacin Najeriya. REUTERS/Akintunde Akinleye

Rahotan binciken ya ji ta bakin matasa 29,9000 da kananan manoma 299 da kuma wadanda suka ci gajiyar fara noman 110 domin gano matsalolin da ake fuskanta.

Ifedi tace sanya matasa da dama cikin aikin noma da samar da abinci na da matukar muhimmanci wajen farfado da tattalin arzikin kasashen Afirka da kuma inganta rayuwar manoman.

A karshe rahotan ya bada shawarar yadda za’a shawo kan matsalolin da aka fuskanta da suka hada da samun jari da horo da fili domin gudanar da aikin noman da kuma rungumar amfani da na’urorin zamani ga kananan manoma a farashi mai rahusa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.