Isa ga babban shafi
Najeriya-Noma

Wata kungiya ta samu tallafin Dala miliyan 5 don taimaka wa manoma a Najeriya

Kungiya mai zaman kanta ta Babban Gona dake Najeriya, ta samu rancen dala miliyan 5 daga Majalisar Dinkin Duniya don taimaka wa kananan manoma, matakin da ake sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen matsalar karancin abinci da rashin ayyukan yi.

Aikin noma da shanu, wanda aka fi yi a yankunan arerwacin Najeriya da wasu sassan Afirka.
Aikin noma da shanu, wanda aka fi yi a yankunan arerwacin Najeriya da wasu sassan Afirka. © RFI/ Sébastien Németh
Talla

Shugaban Asusun Majalisar Dinkin Duniya kan ci gaban Noma (IFAD) Gilbert F. Houngbo ne ya jagoranci kaddamar da sabon shirin samar da kudaden tallafin da zummar fadada kokarin magance matsalar yunwa da talauci a kasashe matalauta, ta hanyar inganta matakan samar da abinci.

Bangaren asusun majalisar dinkiin duniyar na IFAD mai suna PSFP dake tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu ya sanar da bada tallafin bashin farko na dalar Amurka miliyan 5 ga Babban Gona kungiya mai zaman kanta dake Najeriya, sakamakon kokarin da ta yi wajen tallafawa daruruwan kananan manoma wajen fadada ayyukan noman da suke yi zuwa kaiwa matakin na kasuwanci.

An dai kiyasta cewar tallafin bashin na dala miliyan 5, zai baiwa kungiyar ta Babban Gona damar tallafawa kananan manoman Shinkafa da Masara dubu 377 a Najeriya ta fuskokin samar da kayan aiki, bayar da horo da kuma sayan amfanin gonar da manoman suka samar, shirin da ake sa ran zai samar da guraben ayyukan yi akalla dubu 65 da mata zalla, da kuma wasu karin guraben ayyukan yin kimanin dubu 66 ga matasa nan da shekarar 2025.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.