Isa ga babban shafi
ZUBA-JARI

Yan kasuwar Faransa sun gana da Gwamna Lalong da Ayade akan noma

Gwamnonin Jihohin Plateau da Cross Rivers dake Najeriya sun gana da tawagar Yan kasuwa daga Faransa dake ziyarar kasar domin tattauna batutuwan zuba jari musamman abinda ya shafi noman dankalin turawa da dangogin sa.

Gwamnan Cross River Ben Ayade da Gwamnan Plateau Simon Lalong da Jakadan Faransa a Najeriya Jerome Pasquer
Gwamnan Cross River Ben Ayade da Gwamnan Plateau Simon Lalong da Jakadan Faransa a Najeriya Jerome Pasquer © Plateau Government
Talla

Yayin da yake tsokaci lokacin ganawar tare da Jakadan Faransa a Najeriya Jerome Pasquer, Gwamnan Plateau Simon Lalong yayi bayani akan ganawar da suka yi da Paquer a watan Janairun bana dangane da hadin kai da kuma zuba jari, inda suka tabo batutuwa da dama da suka hada da noma da hakar ma’adinai da yawon bude ido da kuma ilimi.

Lalong yace duk da matsalar da ake fama da ita ta annobar korona, Pasquer ya taka rawa wajen ganin Yan kasuwar sun ziyarci Najeriya domin ganewa idon su albarkatun da ake da su da kuma tattaunawa akai tare da Gwamnonin Jihohin guda biyu.

Gwamnan Plateau Simon Lalong na bayani ga Jakadan Faransa Jerome Pasquer tare da tawagar sa
Gwamnan Plateau Simon Lalong na bayani ga Jakadan Faransa Jerome Pasquer tare da tawagar sa © Plateau Government

Gwamnan ya shaidawa Yan kasuwar cewar Jihar Plateau zata gudanar da taron tattalin arziki da zuba jari a watan gobe wanda zai bada damar bude kofofin ta ga Yan kasuwa da masu zuba jari daga ko ina tare domin ganin an bunkasa tattalin arzikin Jihar da kuma Najeriya baki daya.

Jakadan Faransa a Najeriya Jerome Pasquer ya tabbatarwa Gwamnonin guda biyu cewar Yan kasuwar da suka ziyarci Najeriya daga Faransa na duba yiwuwar zuba jari ne a bangaren noman dankalin turawa ta hanyar yadda za’a killace shi da kasuwancin sa tare da wasu ganyayyakin da suke da tsada a kasashen duniya.

Gwamnan Plateau Simon Lalong tare da tawagar Yan kasuwar Faransa
Gwamnan Plateau Simon Lalong tare da tawagar Yan kasuwar Faransa © Plateau Government

Pasquer yace suna duba hanyoyi da dama da zata kaiga bangarorin guda biyu sun ci gajiyar shirin.

Bayan ganawar da akayi a ofishin Jakadancin Faransa dake Abuja, ana saran tawagar Yan kasuwar da jami’an ofishin Jakadancin Faransa zasu ziyarci Jihohin domin ganewa idanun su da kuma ci gaba da tattaunawa.

Jihar Plateau na daga cikin jihohin Najeriya dake da arzikin noma da ma’adinan karkashin kasa da suka hada da kuza da kalambaye da kuma man fetur da aka gano a yan kwanakin nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.