Rikicin manoma da makiyaya ya lakume rayukan mutane 22
Hukumomin kasar Chadi sun ce mutane akalla 22 suka rasa rayukansu a kasar, sakamakon fadan da ya barke tsakanin wasu manoma da makiyaya a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Gwamnan lardin Hadjer-Lamis Amina Kodjiana ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, rikicin ya samo asali ne kan mallakar filaye tsakanin bangarorin biyu a kauyen Zohana mai nisan kilomita akalla 200 daga birnin N’Djemena.
Gwamnar ta ce wasu mutane 18 sun jikkata a tashin hankalin, yayin da kakakin gwamnatin Chadi Abdramane Koumallah yace an tura karin sojoji wurin domin tabbatar da tsaro.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin Sahel ya dade yana haifar da tashin hankalin da ke lakume rayuka da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu