Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Nnamdi Kanu na fama da yunwa - Lauya

Lauyan dake kare shugaban haramcaciyar kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya, Nnamdi Kanu, ya bayyana cewar wanda yake karewar na fama da yunwa a ofishin Hukumar DSS ta kasa da ake tsare da shi.

Shugaban Yan aware Nnamdi Kanu
Shugaban Yan aware Nnamdi Kanu AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Lauyan yace tun daga ranar lahadi Kanu bai ci abinci ba, amma kuma yana nan akan bakar sa na kare muradun da ya sa a gaba.

Lauyan Kanu Ifeanyi Ejiofor yace Hukumar DSS taki mutunta umurnin da kotu ta bayar na tabbatar da cewar Kanu ya samun jin dadin da yake bukata a inda ake tsare da shi.

Sanarwar da Ejiofor ya rabawa manema labarai tace, bayan ziyarar da suka kai masa a inda ake tsare da shi jiya litinin, Mazi Nnamdi Kanu ya aike da sakon fatan alheri ga miliyoyin magoya bayan sa akan yadda suke tare da shi.

 Nnamdi Kanu tare da lauyoyin sa
Nnamdi Kanu tare da lauyoyin sa AFP - KOLA SULAIMON

Ejiofor yace sai dai abin bakin ciki shine, sun fahimci Hukumar DSS taki mutunta umurnin da kotu ta bayar na bashi kular da ta dace, yayin da Kanu ya shaida musu cewar tun ranar lahadi bai ci abinci ba.

Sanarwar tace ana azabtar da Kanu ne saboda ya gabatar da korafi a gaban kotu akan yadda ake kula da shi a hannun jami’an tsaron, matakin da tace ya sabawa umurnin kotu.

Lauyan yace gobe zasu sake komawa kotu domin gabatar da sabon korafi akan matakin da suka ce ba zasu amince da shi ba.

Kotu ta bada umurnin tsare Kanu ne bayan kama shi da akayi a Kenya sakamakon tserewa daga kasar lokacin da aka bada belin sa a shekarar 2017.

Jami’an tsaro na tuhumar Kanu da ci gaba da tinzira jama’a da magoya bayan sa suna tada hankali da zub da jini a sassan Najeriya lokacin da ya samu mafaka a Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.