Isa ga babban shafi

Najeriya na tunanin kafa dokar ta baci a Anambra saboda hare-haren IPOB

Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar kafa dokar ta baci a Jihar Anambra sakamakon ci gaba da tabarbarewar tsaro ganin yadda ake zargin ‘yan awaren kungiyar IPOB da ci gaba da kai munanan hare hare wadanda ke kaiga rasa rayuka da kuma asarar dukiyoyi.

Tutar kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra.
Tutar kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana haka lura da yadda hare haren suka karu a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 6 ga watan gobe.

Malami ya ce gwamnati za ta dauki matakan da suka dace wajen ganin an tabbatar da dimokiradiya a jihar da kuma gudanar da zabe kamar yadda ya dace.

Ministan ya ce amma muddin aka samu barazana ga zaman lafiyar kasa da kuma karen tsaye ga dokokin dimokiradiya, toh babu tantama za su dauki matakan da suka dace, ciki har da kafa dokar ta baci, domin kuwa hakkin su ne su tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa, tare da kare dukiyoyin jama’a.

Malami ya ce matsayin su a gwamnatance shi ne za a ci gaba da shirin gudanar da zabe, kuma za su samar da tsaron da ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.