Isa ga babban shafi
Kano-Najeriya

Hukumar haraji ta Kano ta kulle rassan bankin GT 5 da ke jihar

Masu hulda da bankuna yau a Kano da ke Najeriya sun shiga halin kakanikayi sakamakon yadda hukumar tara kudaden haraji ta jihar ta rufe rassan bankunan Guaranty Trust Bank ko kuma GTB har guda 5 saboda abinda ta kira kin biyan haraji.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government
Talla

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne sakamakon umurnin kotu wadda ta bada umurnin saboda yadda bakin GTB yaki tantance harajin da ake bin sa daga shekarar 2014 zuwa 2019 domin biyan gwamnatin jihar.

Rassan da matakin ya shafa sun hada da Bankin da ke kan hanyar Murtala Muhammad Way da Wapa da hanyar Zaria da Bachirawa da kuma France Road.

Daraktan shari’a na hukumar tara kudaden harajin Bashir Yusuf Madobi ya ce sun dauki matakin ne saboda yadda bankin yaki biyan kudin da ake bin sa da ya kai sama da naira biliyan guda da miliyan 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.