Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Hukumar yaki da rashawa na tuhumar Sarkin Kano da badakalar kudi

A Jihar Kano da ke arewacin Najeriya hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ta kaddamar da wani bincike kan masarautar jihar karkashin mai martaba Aminu Ado Bayero, bisa zargin yadda aka sayar da wasu kadarorin masarautar ba bisa ka’ida ba da kudin su ya haura naira miliyan dari biyar. Harwa yau hukumar na zargin masarautar da karkatar da kudaden cinikin da bincike ya gano ba su shiga asusun masarautar ba. Daga Kanon ga rahoton Abubakar Isah Dandago

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare da Gwamna jihar Ganduje.
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero tare da Gwamna jihar Ganduje. RFI Hausa
Talla

A cewar shugaban  Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano Muhuyi magaji, dalilan saba ka’idar da aka gindaya ne tun farko tasakanin gwamnatin da masarauta ya sanya ta kaddamar da binciken, ganin tun da fari an yarjewa masarautar amfani da filin gandun sarkin ne da zummar gina wasu wuraren shakatawa da na sukuwar dawaki, amma kwatsam sai ji ta yi an cefanar ga wani mutum kan kuma babu labarin sanya kudin cikin asusun masarauta.

To sai dai kuma duk kokarin jin ta bakin masarautar ta kano har zuwa lokacin hada wannan rahoto ya ci tura, ganin yadda na yi ta kiran wayar shugaban ma’aikatan fadar Ahamad Ado bayero babu amsa, hakama sakon karta kwanan da na aike masa

Koda ya ke dai a daya bangaren mutumin da ya sayi filayen daga hannun masarautar ta kanon wato Alhaji Yusuf Shu’aibu ya ruga kotu, da bukatar dakatar da Muhuyi Mgajin daga kokarin hanashi amfani da filin daya siya, wanda kotun ta ce kowa ya tsaya a inda ya ke kafun sauraren kara.

Wannan dai na zuwa bayan da aka sha dambarwa tsakanin masarautar ta Kano da alummar unguwar darmanawa kan yunkurin cefanar da wasu filaye da mutun unguwa ke sallar idi a ciki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.