Isa ga babban shafi
Kano-Ambaliya

Kano: Ambaliya ta lalata gonaki fiye da dubu 10 a daminar bara

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano dake Najeriya tace ambaliyar ruwa tayi sanadiyar mutuwar mutane 51 a daminar bara, yayin da ta mamaye gonaki sama da dubu 10 a kananan hukumomi 44 dake fadin Jihar.

Manomi Ali Dan Ladi tsaye cikin gonar sa da ambaliyar ta lalata a yankin masarautar Rimgim dake jihar Jigawa mai makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya.
Manomi Ali Dan Ladi tsaye cikin gonar sa da ambaliyar ta lalata a yankin masarautar Rimgim dake jihar Jigawa mai makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Babban sakataren hukumar Saleh Jili, ya bayyana haka ga tawagar kungiyoyin fararen hula wanda ya shaidawa cewar ambaliyar ta lalata daukacin abincin da aka shuka a gonakin fiye da dubu 10, zalika iftila'in ya raba mutane sama da dubu 46 da muhallansu.

Jili yace a shekarar da ta gabata, bayan ambaliyar da aka samu, an kuma samu gobara har sama da dubu 10 inda yake cewa karancin kudi na matukar illa ga ayyukan da suke yi na kai dauki ga mabukata.

Sakataren hukumar ya bukaci masu hannu da shuni da su kaiwa wasu daga cikin mutanen da wannan iftila’i ya afkawa dauki domin ceto su daga halin da suka samu kan su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.