Isa ga babban shafi
Najeriya - Nijar

Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaben Nijar cikin lumana

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaben Jamhuriyar Nijar cikin kwanciyar hankali, yayin ganawa da shugaban tawagar kungiyar ECOWAS wajen sanya ido a zaben Arch Namadi Sambo. 

Shugabannin kasashen ECOWAS tare da takwaransu na Mali, Ibrahim Boubacar Keita
Shugabannin kasashen ECOWAS tare da takwaransu na Mali, Ibrahim Boubacar Keita Facebook/Femi Adesina
Talla

Buhari yace sun damu kwarai da zaman lafiyar Jamhuriyar Nijar, saboda haka ya bayyana jin dadin sa da yadda aka kammala zaben ba tare da samun tashin hankali ba, kamar yadda masu sanya ido suka tabbatar.

Shugaban ya kuma yabawa Namadi Sambo da tawagar sa ta ECOWAS kan rawar da suka taka wajen ganin kawo masa kyakyawar labarin abubuwan da suka faru.

Yayin jawabin sa, Namadi Sambo yace sun sanya ido a mazabu kusan 400 a fadin kasar, kuma sun gamsu da yadda al’amura suka gudana da yadda aka baiwa kowanne dan kasa damar sauke nauyin sa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Namadi Sambo yace an samu gagarumar cigaba a zagaye na biyu na zaben, sabanin wanda aka gani ranar 27 ga watan Disambar bara.

Rikicin da ya biyo bayan zaben Nijar

Sakamakon zaben Nijar ya haddasa tashin hankali tsakanin magoya bayan Bazoum Mohamed wanda hukumar zaben kasar ta bayyana a wanda ya lashe zaben da kuma dan takarar jam’iyyar adawa Ousmane Mahaman da shima a bangaren guda ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.

Rikicin na zuwa ne kwanaki 4 bayan gudanar da zagaye na 2 na zaben shugabancin kasar da hukumar zaben kasar CENI ta ce dan takarar jam’iyar da ke mulkin kasar Mohamed Bazoum, ne ya lashe kashi 55.75 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada, sakamakon da dan takarar Adawa tsohon shugaban kasar  Ousmane Mahaman ya kalubalanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.