Isa ga babban shafi
Afrika

An kaddamar da aikin layin dogo daga Najeriya zuwa Nijar

A yau talata Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin shimfida layin dogo tsakanin Nigeria zuwa Janhuriyar Nijar wanda aka tsara kashe Dallan Amurka Biliyan 1.96

Kaddamar da aikin layin dogo daga Najeriya zuwa Nijat
Kaddamar da aikin layin dogo daga Najeriya zuwa Nijat RFI Hausa
Talla

Karkashin wannan aiki akwai kananan tashoshi 15 kuma ana sa ran a kammala aikin cikin shekaru uku. A karshen shekara ta 2020,Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da layin dogo na zamani daga Lagos zuwa Ibadan, shekaru 3 bayan kaddamar da aikin don saukaka sufurin jiragen kasa a kasar, aikin da ya lashe tsabar kudi sama da Dala biliyan guda da rabi.

Katafaren kamfanin gine-ginen na China ya gudanar da aikin wanda aka samu tsaikon kammala shi sakamakon annobar korona wadda ta haifar da matsala a kasashen duniya.

A tashin farko jirgin zai dinga zuwa Ibadan ne yana komawa kowacce rana sau guda, kafin daga bisani a fadada aikin sa, kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta sanar.

Shi dai wannan aiki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fara aikin sa, amma sai aka yi watsi da shi, kafin daga bisani shugaba Muhammadu Buhari mai ci ya farfado da shi a shekarar 2017.

Shugaba Buhari ya jaddada aniyar sa na hade wasu daga cikin manyan biranen kasar da hanyar jiragen kasa domin inganta harkar sufuri a cikin kasar.

A shekarar 2018 gwamnatin Buhari ta kaddamar da sufurin jiragen kasa da gwamnatin Goodluck Jonathan ta fara tsakanin Kaduna zuwa Abuja wanda ya taimaka sosai wajen rage matsalar sufuri da kuma kaucewa barayin da suka addabi jama’ar yankin.

Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Safiyanu Ahmed Daiba mazaunin Daura inda aka kaddamar da bukin sa harsashin fara aikin don jin yadda aka yi bukin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.